Matthew 11

1Bayan Yesu ya gama yi wa almajiransa gargadi, sai ya bar wannan wuri, ya tafi biranensu domin yayi koyorwa, da wa’azi. 2Da Yahaya mai baftisma ya ji daga kurkuku irin ayyukan da Yesu ke yi, sai ya aika sako ta wurin almajiransa. 3Ya ce masa. “Kai ne mai zuwa”? ko mu sa ido ga wani.

4Yesu ya amsa ya ce masu, “Ku je ku gaya wa Yahaya abin da ku ka gani da abin da ku ka ji. 5Makafi suna samun ganin gari, guragu na tafiya, ana tsarkake kutare, kurame na jin magana kuma, ana tada matattu, mabukata kuma ana ba su bishara. 6Kuma mai albarka ne wanda baya tuntube sabili da ni.

7Bayan wadannan sun tafi, sai Yesu ya fara wa jama’a jawabi game da Yahaya mai baftisma, yana cewa, “Me ake zuwa gani a jeji - ciyawa ce da iska ke busawa? 8Shin menene kuke zuwa gani a jeji - mutum mai sanye da tufafi masu laushi? Hakika, masu sa tufafi masu laushi suna zaune ne a fadar sarakuna.

9Amma me ku ke zuwa gani, annabi? Hakika ina fada maku, fiye ma da annabi. 10Wannan shine wanda aka rubuta game da shi, ‘Duba, ina aika manzona, wanda za ya tafi gabanka domin ya shirya maka hanya inda za ka bi’.

11Ina gaya maku gaskiya, cikin wadanda mata suka haifa, babu mai girma kamar Yahaya mai baftisma. Amma mafi kankanta a mulkin sama ya fi shi girma. 12Tun daga kwanakin Yahaya mai baftisma zuwa yanzu, mulkin sama yana shan gwagwarmaya, masu husuma kuma su kan kwace shi da karfi.

13Gama dukan annabawa da shari’a sun yi annabci har zuwa lokacin Yahaya. 14kuma in zaku karba, wannan shine Iliya wanda za ya zo. 15Wanda ke da kunnuwan ji, ya ji.

16Da me zan kwatanta wannan zamani? Ya na kamar yara masu wasa a kasuwa, sun zauna suna kiran juna 17suna cewa mun busa maku sarewa baku yi rawa ba, mun yi makoki, baku yi kuka ba.

18Gama Yahaya ya zo, baya cin gurasa ko shan ruwan inabi, sai aka ce, “Yana da aljannu”. 19Dan mutum ya zo yana ci yana sha, sai aka ce, ‘Duba, ga mai hadama, mashayi kuma, abokin masu karbar haraji da masu zunubi!’ Amma hikima, ta wurin aikin ta ake tabbatar da ita.

20Sannan Yesu ya fara tsautawa biranen nan inda ya yi yawancin ayukansa, domin ba su tuba ba. 21“Kaiton ki Korasinu, kaiton ki Batsaida! In da an yi irin ayuka masu ban mamaki a Taya da Sidon! Yadda aka yi a cikinku, da tuni sun tuba suna sanye da tsumma da yafa toka. 22Amma zai zama da sauki a kan Taya da Sidon a ranar shari’a fiye da ku.

23Ke kafarnahum, kina tsammani za a daukaka ki har zuwa sama? A’a za a saukar da ke kasa zuwa hades. Gama in da an yi irin al’ajiban da aka yi a cikin ki a Sodom, da tana nan har yanzu. 24Amma ina ce maku, za a saukaka wa Sodom a ranar shari’a fiye da ku.”

25A wannan lokaci Yesu ya ce, “Ina yabon ka, ya Uba, Ubangijin sama da kasa, domin ka boye wa masu hikima da fahimta wadannan abubuwa, ka bayyana wa marasa sani, kamar kananan yara. 26I, ya Uba gama wannan shine ya yi daidai a gare ka. 27An mallaka mani dukan abu daga wurin Ubana. Sannan babu wanda ya san Dan, sai Uban, babu kuma wanda ya san Uban, sai Dan, da duk wanda ya so ya bayyana masa.

28Ku zo gare ni, dukanku masu wahala da fama da nauyin kaya, ni kuma zan ba ku hutawa. 29Ku dauki karkiya ta ku koya daga gare ni, gama ni mai tawali’u ne da saukin hali a zuciya, sannan zaku sami hutawa ga rayukanku. Gama karkiyata mai sauki ce, kaya na kuma ba shi da nauyi.”

30

Copyright information for HauULB